Tinubu ya rantsar da Ibas a matsayin mai kula da Ribas

Tinubu ya ce dokar ba ta shafi ɓangaren shari’a ba.

Tinubu ya rantsar da Ibas a matsayin mai kula da Ribas

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya rantsar da Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya) a matsayin Mai Kula da Jihar Ribas.

An rantsar da shi ne a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a ranar Laraba.

Naɗin ya biyo bayan ayyana dokar ta-baci a Jihar Ribas da Shugaba Tinubu ya yi a ranar Talata, bayan dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, Mataimakiyarsa, da ’Yan Majalisar Dokokin Jihar.

Bayan ayyana dokar ta-ɓacin, Tinubu ya sanar da cewa Vice Admiral Ibas ne zai jagoranci jihar na tsawon watanni shida.

Yayin jawabinsa, Shugaban Ƙasa ya bayyana cewa dokar ta-ɓacin ba ta shafi ɓangaren shari’a ba, kuma kotuna za su ci gaba da gudanar da aikinsu kamar yadda doka ta tanada.