Tinubu ya rantsar da sabbin ministoci 7

Tinubu ya rantsar da sabbin ministocin bayan sauke wasu daga muƙamansu da ya yi a baya-bayan nan.

Tinubu ya rantsar da sabbin ministoci 7

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya rantsar da sabbin ministoci a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Bayan rantsar da su, Shugaba Tinubu ya ce zai zage damtse wajen ganin tattalin arziƙin Najeriya ya bunƙasa.

Ya ƙara da cewa akwai kyakkyawar hanyar da gwamnatinsa za ta bi wajen ganin ta kyautata rayuwa kowa da kowa.

Shugaban ya bayyana cewa, duk da ƙalubalen da ake fuskanta, yana ci gaba da ƙoƙarin bunƙasa tattalin arziƙin Najeriya.

Ya shaida wa sabbin ministocin cewa ya zaɓo du ne domin taimakawa wajen ceton ƙasar nan.

A ranar 23 ga watan Oktoba, Shugaba Tinubu ya sauke wasu ministoci biyar tare da naɗa wasu sabbi bakwai.

Har ila yau, Tinubu ya sauyawa wasu ministocinsa hukumomin da za su ci gaba da aiki.

Majalisar Dattawa ta amince da sabbin ministocin a ranar 30 ga watan Oktoba.

Sabbin ministocin sun haɗa da Dokta Nentawe Yilwatda a matsayin Ministan Harkokin Jin-Ƙai da Rage Talauci, Muhammadu Maigari Dingyadi a matsayin Ministan Ƙwadago da Ayyuka.

Akwai Bianca Odumegwu-Ojukwu a matsayin Ƙaramar Ministan Harkokin Ƙasashen Waje, Dokta Jumoke Oduwole a matsayin Ministan Masana’antu, Kasuwanci, da Zuba Jari,

Sauran sun haɗa da Idi Mukhtar Maiha a matsayin Ministan Harkokin Dabbobi, Yusuf Abdullahi Ata a matsayin Ƙaramin Ministan Gidaje da Raya Birane, da Dokta Suwaiba Said Ahmad a matsayin Ƙaramar Ministar Ilimi.

NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da CNG

Sanata Barau ya kai ziyarar ta’aziyya a Kano

Mun kusa kawo ƙarshen rikicin manoma da makiyaya — Tinubu

Tsohon shugaban jam’iyyar PDP na Gombe, ya rasu