Tinubu ya rantsar da sabbin ministoci biyu

An gudanar da bikin rantsarwar ne a gaban iyalan ministocin da manyan jami’an gwamnati.

Tinubu ya rantsar da sabbin ministoci biyu

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya rantsar da sabbin ministoci biyu a ranar Litinin a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Sabbin ministocin da aka rantsar sun haɗa da Mista Joseph Olasunkanmi Tegbe, wanda aka naɗa a matsayin Ministan Wutar Lantarki, da kuma Ambasada Sola Enikanolaiye, wanda ya zama Ƙaramin Ministan Harkokin Waje.

An gudanar da bikin rantsarwar ne a gaban iyalan ministocin da manyan jami’an gwamnati.

Naɗin nasu ya biyo bayan murabus ɗin tsohon Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, da kuma tsohon Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, waɗanda suka ajiye mukamansu domin tsayawa takarar gwamna a jihohinsu.

Daga bisani, Majalisar Dattawa ta amince da naɗin sabbin ministocin a ranar 6 ga Mayu, 2026.

Mista Tegbe, ɗan asalin birnin Ibadan na Jihar Oyo, ƙwararre ne a fannin gyare-gyaren tattalin arziki da gudanar da harkokin gwamnati da kamfanoni, inda ya shafe sama da shekaru 35 yana aiki a bangarori daban-daban.

Shi kuma Ambasada Enikanolaiye, ɗan asalin Jihar Kogi, ya yi fice a fannin diflomasiyya, inda ya yi aiki a ofisoshin jakadancin Najeriya da dama a ƙasashen waje, ciki har da Ethiopia, Serbia, Canada da Birtaniya.

Kafin wannan naɗin, Enikanolaiye ya riƙe muƙamin babban mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harkokin ƙetare da dangantakar ƙasashen duniya.