Tinubu ya rantsar da sabon Sakataren Gwamnati
Shugaba Tinubu ya rantsar da tsohon Gwamnan Binuwai, Sanata George Akume a masayin Sakataren Gwamnatin Tarayya
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da tsohon Gwamnan Jihar Binuwai, Sanata George Akume a masayin Sakataren Gwamnatin Tarayya.
Tinubu ya rantsar da Akume ne a Fadar Shugaban Kasa a wani kwarya-kwaryan biki da ka shira, wanda manan mutane, ciki har da tsoffin gwamnoni da masu ci suka halarta.
- Gwamnan Sakkwato ya raba gero ga iyalan da harin ’yan bindiga ya shafa
- DAGA LARABA: Yadda Cire Tallafin Mai Ya Shafi Rayuwarmu —’Yan Najeriya
An rantsar da Akume ne washegarin da Majalisa ta sahale wa shugaban kasa nada mutum 20 a matsayin masu ba shi shawara na musamman.
Mahalarta sun hada da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima; Shugaban Malisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan; Gwamnan Kwara AbdulRahman AbdulRazaq, da Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Folashade Yemi-Esan, sai kuma matar Akume, Regina.
Akume mai shekaru 69, ya zama Gwamnan Binuwai a lokacin yana da shekaru 45 — daga 1999 zuwa 2007.
Bayan saukarsa daga kujerar gwamna ne ya zama dan Majalisar Dattawa yana da shekaru 53 — daga 2007 zuwa 2019.
Yana da shekaru 65, a 2019 ne tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada shi Ministan Ayyuka na Musamman, kafin yanzu Shugaba Tinubu ya nada shi Sakaaren Gwamnai a shekaru 69.