Tinubu ya rattaba hannu kan dokar bai wa dalibai rance

Za a rika ba dalibai bashi mara ruwa, idan sun gama karatu su biya

Tinubu ya rattaba hannu kan dokar bai wa dalibai rance

Shugaban Kasa Bola Tinubu, ya rattaba hannu a kan dokar da za ta bai wa daliban manyan makarantu bashi su yi karatu, su biya daga baya.

Mamba a rusasshen Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Dele Alake ne ya sanar da hakan ranar Litinin.

Ya ce za a rika adana kudaden da za a yi amfani da su wajen aiwatar da shirin ne a lalitar Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, kuma za a rika bayar da su ne kawai ga daliban manyan makarantu masu karamin karfi.

Kudurin dokar dai, ainihi Kakakin Majalisar Wakilai ta tara, Femi Gbajabiamila ne ya gabatar da shi, kuma ya tsallake karatu na uku ne makonni biyu da suka gabata.

Dokar dai ta tanadi bayar da bashi mara ruwa ga daliban manyan makarantu marasa karfi ta hanyar Asusun Tallafa wa Ilimi na Najeriya.

Tsofaffin ma’aikatan Gombe 2,204 sun karɓi giratuti N4.2bn

Bam ya yi ajalin ɗaliban Islamiyya 2 a Abuja 

Mamakon ruwan sama ya haddasa ambaliya a Saudiyya

’Yan sanda sun ceto yara 4 da aka sace daga Bauchi a Anambra