Tinubu ya rattaba hannu kan Kasafin Kudin 2024

Majalisar Tarayya ta yi karin naira tiriliyan daya da doriya a kan adadin kudin da bangaren zartarwa ya tura musu.

Tinubu ya rattaba hannu kan Kasafin Kudin 2024

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu kan Kasafin Kudin shekarar 2024 da muka yi maraba da ita a wannan Litinin din.

Tinubun ya rattaba hannu kan takardun da ke kunshe da bayanan Kasafin Kudin na Naira Tiririliyan 28.87 a gaban Shugabannin Majalisar Dokokin Tarayya da wasu mambobin Majalisar Zartarwa.

Shugaban ya umarci Ministan Kudi, Wale Edun da takwarsansa na Kasafi da Tsare-Tsare, Abubakar Atiku Bagudu da su yi aiki tare da Majalisar Dokokin Tarayya domin tabbatar da sauye-sauyen da aka yi wa Kasafin Kudin.

Wannan dai shi ne Kasafin Kudi na farko da Tinubun ya sanya wa hannu a matsayinsa na shugaban kasar bayan karbar akalar jagoranci a watan Mayun bara.

Daga cikin wadanda suka halarci taron rattaba hannu kan Kasafin Kudin akwai Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio da Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas.

Kazalika, akwai Babban Mashawarci kan Harkokin Tsaro na Kasa, Malam Nuhu Ribadu, Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila, Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Abdullahi Umar Ganduje da kuma Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar Dattawa; Sanata Olamilekan Adeola da sauransu.

A makon da ya gabata ne dai ’yan Majalisar Dattawa da na Wakilai suka amince da Kasafin Kudin da aka kiyasta zai ci kusan naira tiriliyan 27.5

Sai dai ’yan majalisar sun yi karin naira tiriliyan daya da doriya a kan adadin kudin da bangaren zartarwa ya tura musu.

’Yan majalisar sun bayyana cewa sun amince da Kasafin Kudin ne bayan sun yi nazarinsa ciki da bai, kana suka zartar da shi, har ma suka yi kari a wuraren da suka ga ya dace kamar yadda Kundin Tsarin Mulki ya ba su dama.