Tinubu ya sallami Ministan Kudi Wale Edun
Taiwo Oyedele ya zama sabon Ministan Kudi a yayin da Muttaqa Darma ya zama sabon Ministan Gidaje da Raya Birane.
Ministan Kudi, Wale Edun
Shugaban Kasa Bola Tinubu ya sallami Ministan Kudi, Mista Wale Edun da kuma Ministan Gidaje da Raya Birane, Ahmed Dangiwa.
Tinubu ya sallami ministocin daga mijalisar zartaswarsa ne, a wani yunkuri na kawo sauye-sauye da inganta gudanar da aiki a majalisar.
Sanarwar sallamar da Sakataren Gwamnati, George Akume, ya fitar ta hannun kakakinsa, Yomi Odunuga, ta kara da cewa, Shugaba Tinubu ya kuma nada Taiwo Oyedele a matsayin sabon Ministan Kudi da Tattalin Arziki.
Kazalika ya nada Dakta Muttaqha Darma a matsayin sabon Ministan Gidaje da Raya Birane. Ya kuma umarni tsofaffin ministocin da su kammala abubuwan da ya kamata domin mika ragamar ma’aikatun zuwa jami’an da suka dace.
A baya, Oyedele shi ne karamin minsta a ma’aikatar kudi. Kwararre ne kuam a fannin tsare-tsaren kudi, haraji da dangoginsu, wanda ya karanci fannin aikin Akanta a Kwalejin Yada daga 1999 zuwa 2001.