Tinubu ya sanya dokar ta-baci a Jihar Ribas

Tinubu ya dakatar da gwamna Simi Fubara da mataimakinsa da kum mambobin majalisar dokokin jihar

Tinubu ya sanya dokar ta-baci a Jihar Ribas

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Gwamna da mataimakiyarsa da ɗaukacin ’yan Majalisar Dokokin Jihar Ribas, tare da ayyana dokar ta-baci a Jihar.

Tinubu ya kuma ayyana Vice Marshal Ibok-Ete Ekwe Iba a matsayin Kantoman Jihar Ribas, a yayin jawabinsa ga ’yan Najeriya game da harin da aka kai wa bututun man fetur a Jihar.

“Ina amfani da tanadin kundin tsarin mulkin Nijeriya wajen ayyana dokar ta-baci da kuma dakatar da gwamnan da mataimakinsa da zaɓaɓɓun ’yan majalisar na tsawon wata shida, daga yau 18 ga watan Maris, 2025,” in ji shugaban ƙasar.

“Jihar ta tsaya cik tun bayan ɓarkewar rikicin siyasar inda aka tauye wa al’ummar jihar hakkinsu na cin moriyar mulkin dimokuraɗiyya.

“Na yi iyakar bakin kokarina wajen ganin yadda za a magance matsalar to amma duka ɓangarorin sun yi watsi da yunkurin.”

Tinubu na wannan furuci ne jim kaɗan bayan shan ruwa a ranar Talata, ’yan sa’o’i bayan wani zaman gaggawa da ya yi da manyan hafsoshin tsaro.

Wannan na zuwa ne bayan harin da ’yan ta’adda suka kai kan bututun mai na Trans-Niger Pipeline (TNP) da ke yankin Bodo da ke Karamar Hukumar Gokana ta Jihar Ribas.

Mahara sun kai harin ne bayan barazanar yin hakan da suka bayar a makon jiya a sakamakon kara tsanani da rikicin shugaban jihar ya yi tsakanin ’yan majalisar da kuma gwamna Simi Fubara.

Ibok-Ete Ibas shi ne tsohon Babban Hafsan Sojin Ruwa na Nijeriya daga shekarar 2015 zuwa 2021 a zamanin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.