Tinubu ya sanya hannu a kasafin kuɗin 2025 na N54.99trn
A baya Majalisar Dokoki ta amince da kasafin bayan tattaunawa da nazari a kansa.

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sanya hannu kan kasafin kuɗin shekarar 2025 da ya kai Naira tiriliyan 54.99.
A ranar 13 ga watan Fabrairu, 2025, Majalisar Dokoki ta amince da kasafin bayan tattaunawa da nazari a kansa.
- Hukuma ta kama ciyaman kan zargin badaƙalar filin N100m a Kano
- Gwamnatin Sakkwato ta nemi malaman Jami’a su janye yajin aiki
A baya dai, Shugaba Tinubu ya gabatar da kasafin da ya kai Naira tiriliyan 49.7, amma daga bisani aka ƙara adadin kuɗin.
Shugaba Tinubu ya rattaba hannu kan kasafin a ranar Juma’a, a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Kasafin kuɗin na 2025 ya ninka wanda aka yi a bara, wanda ya tsaya a Naira tiriliyan 27.5, da ƙarin kashi 99.96 cikin 100.