Tinubu ya sauya Shugaban Hukumar Tashohin Ruwa

Tinubu ya sallami Mohammed Bello-Koko daga shugabancin Hukumar Tashoshin Ruwa ta NPA.

Tinubu ya sauya Shugaban Hukumar Tashohin Ruwa

Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Abubakar Ɗantsoho sabon Shugaban Hukumar Tashoshin Ruwa ta NPA.

Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban Kasa, Ajuri Ngelale ya fitar a Yammacin wannan Juma’ar.

Naɗin Ɗantsoho na zuwa ne bayan sallamar Mohammed Bello-Koko daga shugabancin hukumar tashoshin ruwa kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Kazalika, sanarwar ta ce Tinubu ya kuma naɗa tsohon Sanatan Ekiti ta Kudu kuma tsohon Ƙaramin Ministan Ayyuka, Dayo Adeyeye a matsayin sabon Shugaban Majalisar Gudanarwar hukumar ta NPA.

Kafin naɗinsa, Ɗantsoho ya riƙe muƙamai daban-daban a hukumar ciki har da muƙamin babban manaja ne hukumar ta NPA.

Dukkan su za su fara aiki ne nan take, kamar yadda sanarwar Fadar Shugaban Kasar ta bayyana.

NCC ta amince wa kamfanonin sadarwa ƙara kuɗin kira da data

Amurka jinsin mace da namiji kaɗai ta sani a hukumance — Trump

An rantsar da Donald Trump a matsayin Shugaban Amurka na 47

Za mu yi gwanjon motoci 891 da muka ƙwace — EFCC