Tinubu ya shafe kwanaki 180 daga cikin 580 da ya yi na mulkinsa a ƙasar waje – Obi

Shugaba Tinubu a shekarar 2023 da 2024 ya ziyarci ƙasashe da bai gaza 16 ba, ciki har da wasu da ya ziyarta fiye da sau ɗaya.

Tinubu ya shafe kwanaki 180 daga cikin 580 da ya yi na mulkinsa a ƙasar waje – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar Leba (LP) a zaɓen 2023, Peter Obi, ya ce a cikin kwanaki 580 da Shugaba Bola Tinubu ya yi yana mulki a ranar 29 ga Disamba, 2024, shugaban ya kwashe sama da kwanaki 180 a ƙasashen waje.

Obi ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da manema labarai a ranar Alhamis a Abuja kan halin da ƙasar ke ciki, inda ya ƙara da cewa Najeriya na buƙatar shugabanci na gari da za a yi koyi a 2025.

Aminiya ta ruwaito cewa, an rantsar da Tinubu a ranar 29 ga Mayu, 2023 kuma ya shafe kwanaki 584 yana mulki ya zuwa ranar 2 ga Janairu, 2025.

Wakilinmu ya kuma ruwaito cewa, a bana, shugaba Tinubu bai fita daga ƙasar waje ba, kasancewar a halin yanzu yana hutu a Jihar Legas, shugaban ƙasar a shekarar 2023 da 2024 ya ziyarci ƙasashe da bai gaza 16 ba, ciki har da wasu da ya ziyarta fiye da sau ɗaya.

Shugaban ya ziyarci Malabo na ƙasar EQuatorial Guinea; Birnin Landan, a Birtaniya (sau huɗu); Bissau, Guinea-Bissau (sau biyu); Nairobi, Kenya; Porto Norɓo, Jamhuriyar Benin; Hague, Netherlands; Pretoria, Afirka ta Kudu; Accra, Ghana; New Delhi a Indiya; Abu Dhabi da Dubai a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa; New York a Amurka; Riyadh a Saudi Arabia (sau biyu); Berlin a Jamus; Addis Ababa a Habasha; Dakar a Senegal da Doha aƘatar.

Daga cikin tafiye-tafiyen da suka haifar da samun moriya har da ta ranar 29 ga watan Agusta da ya yi zuwa birnin Beijing na ƙasar China, inda shugaba Tinubu ya tattauna da takwaransa na ƙasar China, Ɗi Jinping inda daga bisani ya halarci dandalin haɗin gwiwar China da Afirka kafin ya tashi daga ƙasar China zuwa ƙasar Birtaniya, inda ya shafe kwanaki bakwai, kuma ya dawo ranar 14 ga Satumba.

A ranar 2 ga Oktoba, kwana ɗaya da halarci bikin cika shekaru 64 da samun ’yancin kai, Tinubu ya sake barin Abuja zuwa ƙasar Burtaniya domin hutun aiki na mako biyu.

Ya kwashe kwanaki tara a can sannan ya zarce zuwa birnin Paris na ƙasar Faransa domin yin ‘muhimmiyar hulɗa tsakanin ƙasashen’ kamar yadda babban mataimakinsa na musamman kan harkokin siyasa, Ibrahim Masari ya bayyana.

’Yan bindiga sun sace Farfesa, sun nemi N10m kuɗin fansa

Za a ɗauke wutar lantarki na tsawon mako 2 a Abuja

Hukumar tace fina-finai ta dakatar da Samha kan shigar banza

Sakataren Gwamnatin Ondo ya rasu bayan yin hatsarin mota