Tinubu ya tafi Turai kwanaki 19 kafin rantsuwa
Tinubu zai tafi Turai kwanaki 18 gabanin karbar mulkin Najeriya.
Zababben Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi bulaguro zuwa Turai a wannan Laraba domin ziyarar aiki.
Wannan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Zababben Shugaban Kasar, Tunde Rahman ya fitar.
- Aisha Buhari da matar Tinubu sun yi ran gadin Fadar Shugaban Kasa
- Saudiyya ta zartar wa wanda ya kai wa ’yan sanda hari hukuncin kisa
Sanarwar ta ce Tinubu wanda wasu hadimansa suka rufa masa baya zai yi amfani da bulaguron domin lura da shirye-shiryen mika masa mulki da tsare-tsarensa ba tare da wani lamari ya dauke masa hankali ba.
“A yayin ziyarar Zababben Shugaban Kasar zai gana da masu zuba jari da manyan abokan huldar kasuwanci domin samar da damar zuba jari a kasar karkashin mulkinsa da aka shirya sabbin tsare-tsaren kasuwanci,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Gabanin tafiyar tasa, Tinubu ya gana da Honarabul Tajudeen Abbas da Honarabul Benjamin Kalu wadanda jam’iyyar APC ke mara wa baya domin zama Kakakin Majalisar Wakilai da mataimaki.
Ana sa ran Tinubu zai dawo Najeriya gabanin rantsar da shi a matsayin sabon Shugaban Kasa ranar 29 ga watan Mayu.
Tafiyar Tinubun na zuwa ne dai kasa da makonni biyu bayan wani balaguron da ya yi inda ya shafe fiye da wata guda a ketare.
Lamarin dai ya sanya aka rika jita-jitar rashin lafiya ce ta sa ya yi balaguro, zargin da shi kuma ya musanta da cewa yana da koshin lafiyar jan ragamar akalar jagorancin kasar.