Tinubu ya tafi ziyara Faransa

Tinubu zai dawo gida Najeriya a makon farko na watan Fabarairun 2024.

Tinubu ya tafi ziyara Faransa

Tinubu zai yi balaguro

Shugaba Bola Ahmed Tinubu a wannan Larabar ya tashi daga Abuja zuwa birnin Paris na ƙasar Faransa domin wata ziyara ta ƙashin kansa.

Fadar Shugaban Kasar cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Ajuri Ngelale ya fitar ce ta bayyana hakan.

Sanarwar ta ƙara da cewa, shugaba Tinubu zai dawo Najeriya ne a makon farko na watan Fabarairun 2024.

Wannan dai ita ce ziyara ta farko tun bayan zaftare kashi 60 cikin 100 na adadin makarraban da za su rika yi wa Tinubun rakiyar tafiye-tafiye.

Matakin ya shafi dukkan ministoci da manyan jami’an gwamnatin Tinubu ciki har da mataimakin shugaban ƙasa da uwargidan shugaban ƙasa, wadanda su ma ya ba da umarnin rage adadin jami’an da za su riƙa yi musu rakiya.

Aminiya ta ruwaito cewa, yawan wadanda da za su riƙa yi wa shugaban ƙasar rakiya zuwa ƙasashen waje ba za su wuce jami’ai 20 ba, yayin da ’yan rakiyarsa a tafiyar cikin gida ba za su wuce jami’ai 25 ba.

An dawo da wutar lantarki a Kaduna

An kashe ɗan banga da yin garkuwa da ’yan mata 6 a Neja

’Yan fashin teku sun sace jirgin fasinja mutum 11 sun ɓace a Ribas

Jirgin Amurka ɗauke da mutum 10 ya ɓace