Tinubu ya tafi ziyarar aiki a China

Tawagar shugaban ƙasar ta ƙunshi manyan jami’an gwamnati.

Tinubu ya tafi ziyarar aiki a China

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bar Abuja domin zuwa babban birnin China, Beijing a yau Alhamis 29 ga watan Agusta, don wata ziyarar aiki.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ajuri Ngelale ya fitar, shugaban na Nijeriya zai yada zango na ɗan lokaci a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.

A China, Tinubu zai gana da takwaransa Shugaba Xi Jinping sannan kuma zai gana da shugabannin ’yan kasuwa na China a gefen taron haɗin kai na tsakanin ƙasashen Afirka da China.

Fadar Shugaban Kasar ta ce Tinubu zai kuma gana da wakilan manyan kamfanoni da suka haɗa da Huawei da CRCC.

Sanarwar ta ce ganawar da Shugaban zai yi za ta ƙara habaka yarjejeniyar kammala shimfiɗa layin dogo na Ibadan zuwa Abuja wanda babban rukuni ne na aikin shimfiɗa layin dogo daga Legas zuwa Kano.

Manyan jami’an gwamnatin Nijeriya na daga cikin waɗanda suka raka shugaban ƙasar.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya