Tinubu ya taka rawar gani sosai — Buhari

Wannan ba shi ne karon farko da Buhari ke cewa Najeriya na da wahala wajen shugabanci ba.

Tinubu ya taka rawar gani sosai — Buhari

Tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari, ya ce magajinsa, Bola Ahmed Tinubu, yana taka rawar gani sosai tun bayan hawansa mulki watanni tara da suka wuce.

Tsohon shugaban kasar, ya ce Tinubu ya taka rawar gani idan aka yi la’akari da yanayin da ake ciki, amma ya ce Najeriya kasa ce mai wuyar sha’ani.

Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugaban Hukumar Kwastam, Bashir Adewale Adeniyi da wasu jami’an hukumar a Daura a ranar Lahadi.

Tinubu dai ya fuskanci suka kan wasu daga cikin manufofin da ya bijiro da su game da tattalin arziki da suka hada da cire tallafin man fetur.

Wadannan tsare-tsare da sauransu sun haifar da hauhawar farashin kayayyaki, tabarbarewar tattalin arziki, da faduwar darajar Naira, wanda hatta a ‘yan kwanakin nansai da aka yi zanga-zanga a fadin kasar nan.

Buhari ya ce yana da matukar wahala ga ‘yan kasar su iya jure matsin tattalin arziki da ake fama da shi, sai dai ya ce yana goyon bayan manufofi da tsare-tsaren gwamnati mai ci.

“Na gode kwarai da ziyararku. Na yaba sosai. Ina kyautata zaton Tinubu ya yi kokari sosai zuwa yanzu,” in ji Buhari.

“Najeriya tana da sarkakiya sosai. Hakika, da wuya wani ya iya wani abun a zo a gani.”

A nasa jawabin, Adeniyi ya gode wa tsohon shugaban kasar kan rawar da ya taka wajen tabbatuwar Dokar Hukumar Kwastam (NCS) ta 2023.

Har wa yau, shugaban na Kwatsam ya ziyarci mai martaba Sarkin Daura, Dokta Farouk Umar Farouk.

A yayin ziyarar, Adeniyi ya ce “Wannan mataki na doka ya bai wa hukumar Kwastam damar fadada manufofin samar da kudaden shiga da kuma saukaka harkokin kasuwanci, haka kuma ya taimaka sosai ga ci gaban tattalin arzikin Najeriya,” in ji Adeniyi.

Idan dai ba a manta ba, wannan ba shi ne karon farko da Buhari ya yi furuci kan wahalar shugabanci da Najeriya ta ke da shi ga masu rike da akalar jagoranci ba.

A watan Nuwamban 2023, yayin wata hira da gidan talabijin na Najeriya (NTA), Buhari ya ce Najeriya tana da wahalar shugabanci.

“’Yan Najeriya na da wahala wajen shugabanci. Mutane ne da suka san hakkinsu. Suna ganin ya kamata su kasance a wajen ba kai ba. Don haka, suna lura da kusan kowane mataki da aka dauka. Kuma dole ne ka jajirce dare da rana don tabbatar da cewa ka yi kokari sosai,” in ji Buhari.

Wike ya ƙwace filayen jiga-jigan ’yan siyasa a Abuja

Gwamnoni sun ƙi amincewa da ƙara harajin VAT

Matashi ya kashe mahaifinsa kan N5,000 a Delta

Muhimman batutuwa da Biden ya taɓo a jawabin yi wa Amurkawa bankwana