Tinubu ya umarci a taƙaita shagulgulan bikin Ranar ’Yancin Kai ta bana

Matakin na da alaƙa da halin da Najeriya ke ciki, abin da ya sa Tinubu ya ba da umarnin ke nan.

Tinubu ya umarci a taƙaita shagulgulan bikin Ranar ’Yancin Kai ta bana

Shugaba Bola Tinubu ya ba da umarnin a taƙaita shagulgulan bikin Ranar ‘Yancin Kai na Nijeriya na bana da zai gudana a ranar 1 ga watan Oktoba mai kamawa.

Wannan shi ne karo na biyu ke nan a jere Gwamnatin Nijeriya tana ɗaukar wannan mataki la’akari da matsin rayuwa da ake fuskanta a ƙasar.

A hirarsa da manema labarai yayin baje kolin shagulgulan da aka tsara gudanarwa a bana, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume ya ce Gwamnatin Shugaba Tinubu na sane kuma tana tausaya wa ’yan Nijeriya game da halin matsin tattalin arzikin da suke ciki, don haka aka taƙaita shagulgulan da za a gudanar a bikin.

An taƙaita shagulgula a bikin zagayowar ranar samun ‘yancin kan Najeriya na 63 a bara, inda Sanata Akume, ya ce ba za a gayyaci shugabannin ƙasashen ƙetare ba, saboda halin matsin tattalin arzikin da ƙasa ke ciki.

A yayin ganawar ta jiya Alhamis, Akume ya ce an yanke shawarar ne a bisa la’akari da halin da ƙasa ke ciki, don haka Shugaba Tinubu ya amince a taƙaita shagulgula a bikin ‘yancin kan Nijeriya na 64.

Rikicin Masarautar Kano: Tsagin Aminu Ado Bayero zai ɗaukaka ƙara

Yadda Jimmy Carter ya ceto rayuwata – Obasanjo

Sojoji sun lalata sansanin Bello Turji, sun kuɓutar da mutum 7

Wani mutum ya rasu yayin gyaran rijiya a Kano