Tinubu ya umarci Dangote da BUA su rage farashin siminti

Tinubu ya bukaci kamfanonin su rage farashin ne don samar wa talaka sauki.

Tinubu ya umarci Dangote da BUA su rage farashin siminti

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya umarci kamfanin Dangote da BUA da su rage kudin farashin buhun siminti don samar wa al’umma sauki daga matsin rayuwa da ake fuskanta.

Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi ne, ya bayyana hakan ga manema labarai jim kadan bayan ziyara da ya kai masana’antar siminti ta BUA da ke Sakkwato a ranar Alhamis.

Babban Darakta a kamfanin BUA, Alhaji Kabiru, ya ce a halin yanzu suna sayar da buhun siminti kan kudi Naira 6000, don cika alkawarin da suka yi daukar wa shugaban kasa cewa ba za su sayar da buhun siminti sama da 7000 ba.

“Game da batun farashin siminti, zan iya cewa har yanzu suna yin abin da ya dace kamar yadda suka tattauna da shugaban kasa

“Shugaban kasa ya jaddada batun dawo da farashin baya domin saukaka wa talaka.

“Ina so na kara musu kwarin gwiwa don su bi umarnin shugaban kasa domin mu cimma shirin samar da gidaje da kuma sabbin hanyoyin gina rayuwa kamar yadda shugaban kasa ya bukata,” in ji shi.

A baya-bayan nan dai kayayyaki sun yi tashin gwauron zabi a Najeriya, lamarin da ya sanya talakawa kokawa.

Farashin kudin buhun siminti ya ninka kudinsa na baya, inda a wasu jihohi ake sayar da shi daga Naira 10,000 zuwa 15,000.

A makon da ya gabata, Shugaba Tinubu ya gana da shugabannin kamfanonin siminti da ke kasar nan, don tattauna yadda za a daidaita farashin simintin.

A gefe guda kuwa, kungiyoyin kwadago na NLC da TUC sun gudanar da zanga-zangar kwanaki biyu a ranar Talata da Laraba, don neman gwamnatin tarayya yi wani abu kan tsadar rayuwa a Najeriya.

Shugaba Tinubu dai ya roki ‘yan Najeriya da su kara hakuri kan yanayin da ake ciki, wanda a cewarsa yana aiki tukuru don samar wa da talaka sauki daga halin da ake ciki.

Gwamnatin Yobe ta tallafa wa magidanta 53,000 da N3.91bn a 2024

Uwargidan Sanata Goje ta tallafa wa mata da matasa a Gombe

An kama bokaye 2 kan zargin yi wa shugaban Zambiya asiri

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano