Tinubu ya umarci ICPC ta binciki zargin kafa hukumar bogi

Tinubu ya bai wa ICPC kwanaki 30 domin gudanar da bincike da kuma gabatar masa da rahoto.

Tinubu ya umarci ICPC ta binciki zargin kafa hukumar bogi

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) da ta gudanar da binciken kafa Hukumar Inganta Harkokin Ƙasashen Waje (PFIPC) ba bisa ƙa’ida ba.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Talata, ya ce shugaba Tinubu ya bai wa ICPC wa’adin kwanaki 30 ta kammala binciken tare da miƙa masa rahoto.

Sanarwar ta ce Gwamnatin Tarayya ba ta taɓa kafa hukumar PFIPC ba, kuma ba ta da wata doka ko amincewar gwamnati da ta halatta kafuwarta.

Haka kuma, an zargi wani mutum mai suna Adeniyi Adeyemi Matthew da bayyana kansa a matsayin Darakta Janar na hukumar tare da yin iƙirarin cewa shugaban ƙasa ne ya naɗa shi.

Binciken zai haɗa da zargin amfani da takardun naɗin aiki na bogi da wasu takardun gwamnati na bogi, da amfani da sunan shugaban ƙasa wajen neman amincewar hukumomi da sauƙaƙa samun biza, da kuma buɗe asusun banki da sunayen wasu hukumomin gwamnati ta hanyar amfani da takardun bogi.

ICPC za ta kuma binciki duk wanda ake zargin ya taimaka ko ya taka rawa wajen wannan lamari, ciki har da jami’an gwamnati, cibiyoyin kuɗi da sauran waɗanda ake zargin na da hannu.

Shugaba Tinubu ya kuma umarci hukumar da ta gano giɓin da ke cikin tsarin gwamnati da ya bai wa wannan hukumar damar gudanar da ayyukanta, tare da ba da shawarwarin yadda za a hana faruwar irin wannan lamari a gaba.

Har ila yau, shugaban ya umarci dukkanin ma’aikatu, hukumomi da sassan gwamnatin tarayya su bai wa ICPC cikakken haɗin kai domin kammala binciken.

Tinubu ya jaddada cewa dole ne a kare mutuncin Fadar Shugaban Ƙasa da hukumomin gwamnati daga irin wannan katoɓara.