Tinubu ya ware N26trn a kasafin 2024
Kasafin farko da Tinubu zai gabatar ya haura na Buhari da tiriliyan 5.2 a daidai lokacin da darajar Naira ta yi faduwa mafi muni a tarihi
Gwamnatin Tarayya na shirin gabatar da Naira tiriliyan 26 a matsayin kasafin shekarar 2024.
Ministan Kasafi da Tsare-tsare, Sanata Atiku Bagudu, ya sanar bayan Taron Majalisar Zartarwa ta Kasa da Shugaba Tinubu ya jagoranta cewa ɓangaren zartaswa zai gabatar wa Majalisa kasafin na 2024 domin amincewa zuwa ranar 31 ga watan Disambar 2023.
- ’Yan bindiga sun yi garkuwa, sun kashe mutane da dama a ƙauyen Kano
- Tsadar rayuwa ta yi tashi mafi girma cikin shekaru 20 a Najeriya
Kasafin na 2024, wanda shi ne na farko da Gwamnatin Tinubu za ta gabatar, ya haura na 2023 na Naira tiriliyan 21.8 da tsohuwar Gwamnatin Buhari ta gabatar wa Majalisa da tiriliyan 5.2.
Tsadar rayuwa a Najeriya
Ko da yake Bagudu bai bayyana alkaluman da aka dogara da su wajen yin hasashe a kasafin na 2024 ba.
Amma dai kasafin farko da Tinubu zai gabatar zai zo ne bayan darajar Naira ta yi faduwa mafi muni a tarihi, inda Dala ɗaya ta haura Naira 1,000.
Haka kuma farashin danyen mai wanda shi ne babban abin samun kudin shigar da kasar ta dogara da shi na ci gaba da tashi a kasuwar duniya.
Sai dai kuma farshin tataccen mai a ƙasar mai arzikin danyen mai ya ninninku tun bayan da Tinubu ya fara sanar da soke biyan tallafin mai a ranar 29 ga watan Mayu da ya karbi rantsuwar kama aiki.
Ko da yake daga bisani gwamnatin ta sanar cewa ta dawo ta ci gaba da biyan tallafin domin rage tsadarsa ga ’yan Najeriya.
Tun lokacin da Tinubu ya sanar da soke tallafin mai kayayyaki suka yi tashin gwauron zabo da kimanin kashi 100 a Najeriya.
Hakan ya haifar da zanga-zangar ƙungiyar ƙwadago don neman ƙarin albashin ma’aikata ko kuma dawo da tallafin.
A jawabinsa ga ’yan Najeriya a ranar zagayowar samun ’yancin kasar a ranar 1 ga watan Oktoba da muke ciki, Tinubu — wanda a baya ya ce za a yi amfani da kudin da ake kashewa kan tallafin mai wajen inganta abubuwa more rayuwa —ya sanar da karin wasu matakai da gwamnatinsa za ta dauka domin rage raɗaɗin cire tallafin.
Matakan sun hada da biyan ma’aikata karin albashi na wucin gadi na tsawon wata shida kafin cim-ma matsaya kan sabon mafi ƙarancin albashi.
Tuni dama gwamnatin ta ware tallafin kudi da kayan abinci na Naira biyan biyar ga kowace jiha da birnin tarayya, ta kuma ba su kashin farko na kudi da hatsi domin raba wa jama’a.
Hakazalika ya yi alkawarin samar da motocin sufuri mai rangwame ga ma’aikata, da kuma shirin mayar da motoci masu amfani da man fetur su koma shan man dizel.
Haka kuma, gwamnati ta ba da damar rage yawan ranakun zuwa aiki ga ma’aikata; da dai sauran matakai.
Sai dai zuwa wannan lokaci, matakan ba su share hawayen ’yan Najeriya ba, a yayin da matsaloli suka dabaibaye wasu daga cikin matakan.
A yayin da take kasa tana dabo, abin jira a gani shi ne alkaluman kasafin, kason da aka ware wa bangarori, yiwuwar aiwatar da shi da ma irin tasirin da zai yi sabanin abin da aka saba gani.