Tinubu ya yaba wa NNPCL kan farfaɗo da matatar mai ta Fatakwal
Tinubu ya jinjina wa Buhari kan yadda ya fara aikin matatar a lokacin mulkinsa.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya yaba wa Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL), kan farfaɗo da matatar mai ta Fatakwal, wadsa ta fara aiki.
Ya kuma gode wa tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, kan fara gyaran matatar man da sauran matatun mai a faɗin Najeriya.
Tinubu ya jinjina wa Bankin African Export-Import kan tallafin kuɗin da ya bayar don gudanar da aikin matatar.
A wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar, ya ce Tinubu ya jinjina wa Shugaban NNPCL, Mele Kyari, bisa jajircewarsa da ƙoƙarinsa wajen tabbatar da wannan nasarar.
Shugaban, ya buƙaci NNPCL da ya hanzarta wajen farfaɗo da sashe na biyu na matatar Fatakwal, da matatun Warri da Kaduna.
“Wannan ƙoƙari zai ƙara yawan kayayyakin da ake sarrafawa a cikin gida, za su taimaka tare da matatun mai masu zaman kansu, kuma za su ciyar da Najeriya gaba a ɓangaren makamashi a duniya.
“A ɓangaren iskar gas za a samu ci gaba ƙarƙashin wannan gwamnati,” in ji Tinubu.
Tinubu ya jaddada burinsa na gyara matatun mai na Najeriya don kawo ƙarshen halin da ake ciki a ƙasar nan.
Ya kuma yi kira ga duk wanda aka ɗora wa nauyi da ya ci gaba da mayar da hankali tare da yin aiki bisa gaskiya da amana.
Shugaban ya yi alƙawarin cewa gwamnatinsa za ta yi aiki don wadata ƙasa da makamashi.