Tinubu ya yi alhinin rasuwar tsohon shugaban PDP, Audu Ogbeh

Ogbeh ya rasu yana da shekaru 78 a duniya.

Tinubu ya yi alhinin rasuwar tsohon shugaban PDP, Audu Ogbeh

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga jama’a da Gwamnatin Jihar Binuwai bisa rasuwar tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Cif Audu Ogbeh.

Ya kuma yi wa iyalansa, abokansa da dukkanin ’yan uwansa ta’aziyya kan rashin da suka yi.

Cif Ogbeh, ya rasu yana da shekaru 78 a duniya, ya hidimta wa Najeriya a ɓangarori daban-daban ciki har da Ministan Sadarwa a lokacin Jamhuriya ta Biyu.

Sannan daga baya ya zama Ministan Noma a Gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari.

A cewar sanarwar Bayo Onanuga, mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labaru, Ogbeh mutum ne mai basira da zurfin tunani wanda ya taimaka wajen tsara manufofin gwamnati da magance manyan matsalolin ƙasa.

Ogbeh, ya fara harkar siyasa a shekarun 1970 a matsayin ɗan majalisa, sannan daga baya ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa jam’iyyar APC.

Shugaba Tinubu, ya bayyana shi a matsayin “Ɗan ƙasa wanda hikimarsa, jajircewarsa, da ƙoƙarinsa na ci gaba suka bar tarihi a siyasar Najeriya.

“Kullum yana da hujjoji da alkaluma don kare ra’ayinsa. Ƙasa za ta yi matuƙar kewar gogewarsa.”

Shugaban ya yi addu’ar Allah Ya jiƙansa ya kuma bai wa iyalansa haƙuri da juriya.