Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Daniel Bwala dai tsohon hadimi ne ga tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Atiku Abubakar.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Tinubu tare da Daniel Bwala

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin Daniel Bwala a matsayin mashawarcinsa na musamman kan harkokin yaɗa labarai.

Mai magana da yawun shugaban ƙasar Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin ranar Alhamis.

Daniel Bwala dai tsohon hadimi ne ga tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Atiku Abubakar.

Onanuga ya kuma sanar da naɗin wasu sabbin muƙamai da Shugaba Tinubu ya tabbatar da suka haɗa da Mista Olawale Olapade a matsayin Darekta-Janar na Hukumar Wasanni da Dokta Abisoye Fagade a matsayin Darekta-Janar na Hukumar Karɓar Baƙi da Yawon Buɗe Ido.

Haka kuma, hadimin shugaban ƙasar ya sanar da naɗin Dokta Adebowale Adedokun a matsayin Darekta-Janar na Hukumar Da ke sa ido kan saye-sayen Gwamnati.

 

Yadda dagacinmu ya sassara ni da adda — Maraya

Bidiyoyin da suka ɗauki hankalin ’yan Najeriya a 2024

An kama mutum 859 da ceto 46 da aka yi garkuwa da su a Filato – ’Yan sanda

Sojoji sun kashe shahararren ɗan bindiga a Zamfara