Tinubu ya yi sauyi a shugabannin Hukumar Raya Arewa maso Yamma
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi sauye-sauye a jerin shugabannin sabuwar Hukumar Raya Arewa maso Yamma da ya naɗa a bayan nan. A makon nan ne Shugaba Tinubu ya tura sabon jerin sunayen mambobin hukumar ta kula da ci gaban Arewa maso Yamma (NWDC) zuwa Majalisar Dattawa domin amincewa. Yadda jadawalin FIFA Club World Cup […]
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi sauye-sauye a jerin shugabannin sabuwar Hukumar Raya Arewa maso Yamma da ya naɗa a bayan nan.
A makon nan ne Shugaba Tinubu ya tura sabon jerin sunayen mambobin hukumar ta kula da ci gaban Arewa maso Yamma (NWDC) zuwa Majalisar Dattawa domin amincewa.
- Yadda jadawalin FIFA Club World Cup na bana ya kasance
- Yarjejeniyar zaman lafiya da ’yan bindiga ta faranta wa mazauna Birnin Gwari
A cikin sanarwar da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Juma’a, ya bayyana cewa an maye gurbin wasu daga cikin sunayen da aka fara turawa.
Shugaban da aka zaɓa yanzu shi ne Alhaji Lawal Sama’ila Abdullahi da ya maye gurbin Ambasada Haruna Ginsau, sai kuma Farfesa Abdullahi Shehu Ma’aji wanda zai ci gaba da riƙe muƙamin Darakta Janar.
Kazalika, Tinubu ya naɗa Emeka Atuma a matsayin Shugaban Hukumar Ci Gaban Kudu maso Gabas (SEDC), kuma ya tura sunayen wasu mambobin na NWDC daga yankuna daban-daban na Nijeriya.
Sabbin sunayen wakikai daga yankuna shida na ƙasar waɗanda za su zama mambobi a Hukumar ta NWDC sun haɗa da Chukwu Chijioke da Ahmed Mohammed da Injiniya Ahmed Rufai Timasaniyu da Macdonalds Michael Uyi da Yemi Ola sai kuma Honarabul Babatunde Dada.