Tinubu ya yi ta’aziyyar rasuwar Sarkin Ningi

Sarkin ya rasu da sanyin safiyar ranar Lahadi.

Tinubu ya yi ta’aziyyar rasuwar Sarkin Ningi

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya jajanta wa al’ummar Masarautar Ningi da Gwamnatin Jihar Bauchi game da rasuwar Sarkin Ningi, Alhaji Yunusa Danyaya.

A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale ya fitar, ya ce basaraken mai daraja ta ɗaya ya rasu da sanyin safiyar Lahadi.

“Shugaba Tinubu ya bayyana marigayin a matsayin haziƙin shugaba wanda ya yi amfani da mulki domin amfanin al’ummarsa.

“Shugaban Ya yi addu’ar Allah ya jiƙan marigayin, ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ga iyalansa da kuma al’ummar masarautar Ningi,” in ji Ngelale.

Sarkin ya rasu ne da safiyar ranar Lahadi, ya rasu yana shekara 88 a duniya.

Wike ya ƙwace filayen jiga-jigan ’yan siyasa a Abuja

Gwamnoni sun ƙi amincewa da ƙara harajin VAT

Matashi ya kashe mahaifinsa kan N5,000 a Delta

Muhimman batutuwa da Biden ya taɓo a jawabin yi wa Amurkawa bankwana