Gwamnati ta yi wa ma’aikata da ’yan fansho karin albashi

’Yan fansho ma sun samu karin albashi kuma duka karin zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Janairu. 2024.

Gwamnati ta yi wa ma’aikata da ’yan fansho karin albashi

Gwamnatin Tarayya ta yi wa ma’aikatanta karin albashi da kashi 25% zuwa kashi 35%.

Kazalika gwamnatin ta yi wa ’yan fansho karin kashi 20% zuwa kashi 28% a kan albashinsu na yanzu.

Sanarwar da kakakin hukumar albashi ta kasa, Emmanuel Njoku, ya fitar ranar Talata, ta ce duk karin albashin da gwamnati ta yi zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Janairu, 2024.

Ma’aikatan da aka yi wa karin albashi sun hada da masu karbar albashi na bai-daya, wato Consolidated.

Wannan karin albashi na zuwa ne a jajabirin bikin Ranar Ma’aikata ta Duniya ta bana.

Kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) dai ta dade tana neman a yi wa ma’aikata karin albashi, bisa la’akari da yadda abubuwan masarufi suka yi tashin gwauron zabo a ƙasar tun bayan da gwamnati ta sanar da janye tallafin mai a ranar 29 ga Mayu, 2023 da aka rantsar da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu.

Aminiya ta ruwaito cewa kungiyar ma’aikatan jami’a ta  bayyana cewa mambobinta ba za su amince da mafi ƙarancin albashin da ya faza Naira dubu 300 ba.

Kawo yanzu dai ƙungiyoyin ba su ce komai kan karin albashin ba.

A ranar Laraba da safe ake sa ran shugaban kasa zai yi jawabi ga ’yan Najeriya albarkacin zagayowar Ranar Ma’aikata.

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta