Tinubu ya zama dan takarar shugaban kasar APC

Tinubu ya yi wa sauran ’yan takarar tikitin shugaban kasa a APC fintinkau

Tinubu ya zama dan takarar shugaban kasar APC

Bola Ahmed Tinubu

Tsohon Gwaman Jihar Legas, Asiwaju Bola Tinubu, ya zama dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya a zaben 2023.

Tinubu ya lashe zaben ne bayan ya kere sauran abokan karawarsa da mafi yawan kuri’un da daliget sama da 2,00o suka jefa a zaben fidda gwanin da jam’iyyar ta gudanar a ranar Laraba.

Zuwa lokacin hada wannan rahoton, Tinubu na da kuri’a sama 1,000 a yayin da mai bi mishi, tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi ke bi mishi da kuri’a 316.

Tun kafin gudanar da zaben, mutum bakwai daga cikin mutum 23 da ke neman tikitin a karkashin inuwar jam’yyar, suka janye wa Tinubu.

Suran ’yan takarar da kuri’un da suka samu sun hada da tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Ahmad Sani Yerima wanda ya samu  kuri’a hudu.

Kuri’un da sauran ’yan takarar suka samu zuwa yanzu su ne:

  1. Chubuike Rotimi Amaechi, tsohon Ministan Sufuri – 316
  2. Farfesa Yemi Osinbajo, Matamakin Shugaban Kasa, – 235
  3. Sanata Ahmad Lawan, Shugaban Majalisar Dattawa – 152
  4. Yahaya Bello, Gwamnan Jihar Kogi – 47
  5. David Umahi, Gwamnan Jihar Ebonyi – 38
  6. Ben Ayade, Gwamnan Jiyar Kuro Riba – 37
  7. Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Ahmed Sani Yerima – 4
  8. Chukwuemeka Nwajiuba, tsohom Minista a Ma’aikatar Ilimi – 1
  9. Dokta Christopher Onu – 1
  10. Sanara Rochas Okorocha, tsohon Gwamman Jihar Imo – 0
  11. Fasto Tunde Bakare, tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa – 0
  12. Tien Jack-Rich – 0
  13. Abasi Ikoli – 0

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno