Tinubu ya fadi a mota a dandalin Eagle Square
Muƙarrabansa sun tallafo shi bayan ya faɗa cikin motar.
Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya fadi bayan da ya zame a yayin hawa motar da za ta kai shi wajen faretin sojoji a dandalin Eagle Square da ke Abuja, a lokacin bikin zagayowar Ranar Dimokuraɗiyya.
Shugaban wanda ya yi wa ’yan Najeriya jawabi a talabijin, ya isa dandalin Eagle Square domin faretin da safiyar ranar Laraba.
- ’Yar Najeriya ta haifi jaririn farko a Hajjin 2024
- Zan aike wa majalisa ƙudirin ƙarin mafi ƙarancin albashi —Tinubu
Tuni sojoji da wasu muƙarrabansa suka tallafa masa ya sake tashi domin tsayawa a cikin motar.
Tinubu na sanye da farar babbar riga lokacin da ya faɗi a cikin motar, wanda daga bisa wasu hadimai suka ɗago shi ya tashi.
Bayan ya tashi komai ya daidaita an ci gaba da faretin yayin da shugaban ƙasar ya dinga ɗaga wa jama’a hannu yayin da motar ta ke tafiya a hankali.