Tinubu ya zarce Faransa daga Birtaniya

A ranar 2 ga watan Oktoba ne Tinubu ya tafi Birtaniya domin yin hutun mako biyu, kamar yadda fadarsa ta bayyana a lokacin, amma ba ta ce zai je Faransa ba.

Tinubu ya zarce Faransa daga Birtaniya

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya wuce birnin Paris na Faransa daga birnin Landan na Birtaniya a yau Juma’a.

Mashawarcin shugaban ƙasa kan harkokin siyasa, Ibrahim Kabir Masari ne ya bayyana hakan bayan ya kai masa ziyara a Landan.

“Yau na yi nasarar kai wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ziyara a gidansa da ke Birtaniya, inda muka yi tattaunawa mai amfani,” in ji shi cikin wani saƙo a shafinsa na X.

“Daga nan kuma sai muka wuce birnin Paris na Faransa domin yin wasu ayyukan masu muhimmanci.”

Aminiya ta ruwaito cewa, a ranar 2 ga watan Oktoba ne Tinubu ya tafi Birtaniya domin yin hutun mako biyu, kamar yadda fadarsa ta bayyana a lokacin, amma ba ta ce zai je Faransa ba.

Ta ce, zai koma gida da zarar hutun ya ƙare.

Wannan dai shi ne karon farko da shugaba Tinubu ya ɗauki hutu tun bayan hawansa mulki a watan Mayun 2023, duk da cewa ya yi tafiye-tafiyen ƙasashen waje da dama daga lokacin zuwa yanzu.

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya

Kano: Kwamishinan da Abba ya tsige ya koma Jam’iyyarAPC