Tinubu ya zargi Oyegun da bata masa aiki

Jagoran Jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ya rubuta wa shugaban jam’iyyar APC ta kasa John Odigie-Oyegun wasika ta musamman inda ya zargi shugaban jam’iyyar da bata masa aiki kamar yadda The Cable ta ruwaito.   Tinubu ya aike wa Oyegun da wasikar sannan kuma ya aike Shugaban Kasa da Mataimakinsa da Shugaban Majalisar Dattawa da […]

Tinubu ya zargi Oyegun da bata masa aiki

Jagoran Jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ya rubuta wa shugaban jam’iyyar APC ta kasa John Odigie-Oyegun wasika ta musamman inda ya zargi shugaban jam’iyyar da bata masa aiki kamar yadda The Cable ta ruwaito.

 

Tinubu ya aike wa Oyegun da wasikar sannan kuma ya aike Shugaban Kasa da Mataimakinsa da Shugaban Majalisar Dattawa da takwaransa na Majalisar Wakilai.

 

A kwanakin baya ne dai Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada Bola Tinubu domin ya jagoranci sulhu tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar a duk fadin Najeriya.

 

A wasikar, Bola Tinubu ya ce maimakon shugaban jam’iyyar ya tallafa masa kamar yadda ya yi alkawari, sai dai ya zama mai bata masa aiki.