Tinubu yana zagayawa da daddare, ya san mutane suna shan wahala – Kalu
A wasu lokuta shugaban ya kan kewaya cikin garin Abuja da daddare domin sanin halin da ake ciki.
Sanata Orji Uzor Kalu ya ce, shugaban Ƙasa Bola Tinubu yana da masaniya kan matsalolin tattalin arzikin da ’yan Nijeriya ke ciki.
A tattaunawarsa da tashar talabijin ta Channels TV a shirin siyasa na Politics Today, ya ce shugaban yana ɗaukar matakan shawo kan lamarin.
Ya yi iƙirarin cewa, a wasu lokuta shugaban yakan kewaya cikin garin Abuja da daddare domin sanin halin da tattalin arzikin ƙasar ke ciki.
Kalu ya ce, “Shugaban da kansa ya san cewa ’yan Nijeriya na cikin wahala da yunwa. Shi ma ya san garin sosai.
“Shugaban ƙasa a wasu dare yana amfani da motarsa ya zagaya ya san abin da ke faruwa a nan Abuja.”
Kalu ya bayar da hujjar cewa matsalar tattalin arziki ba Nijeriya kaɗai ba ce, ya ƙara da cewa har yanzu ƙasashe da dama na fama da matsin rayuwa tun bayan ɓullar annobar COVID-19.
A cewarsa, dalilin da ya sa wasu ƙasashe ba za su ji matsin tattalin arziki kamar Nijeriya ba, shi ne daidaituwar tattalin arzikin da suke da shi.