Tinubu zai ƙaddamar da ayyuka a Yobe
Abdullahi Bego ya ce dukkan shirye-shirye sun kammala don karɓar mai girma shugaban ƙasar a yau Asabar.
A wannan Asabar ce ake sa ran Shugaba Bola Ahmad Tinubu zai kai ziyara Jihar Yobe domin buɗe wasu muhimman ayyukan raya ƙasa da Gwamna Mai Mala Buni ya aiwatar.
Da ya ke jawabi ga manema labarai a babban ɗakin taro na Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Jihar (NUJ) da ke Damaturu, Kwamishinan Harkokin Cikin Gida, Yaɗa Labarai da Al’adu, Alhaji Abdullahi Bego ya ce dukkan shirye-shirye sun kammala don karɓar mai girma shugaban ƙasar a yau Asabar.
- DSS ta kama mutumin da ya yi garkuwa da mahaifiyar Rarara
- Muna maraba da El-Rufa’i a Jam’iyyar NNPP — Kwankwaso
A cewarsa, shugaban ƙasar zai ƙaddamar da ba da tallafin kayan aikin gona na biliyoyin Naira ga manoman Yobe.
Ya yi bayanin cewa Gwamna Mai Mala Buni ya tanadar wa manoman jihar kayayyakin bunƙasa harkokin noma musamman saboda akasarin al’ummar Yobe manoma ne.
Kwamishinan ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnatin Mai Mala Buni za ta ci gaba da gudanar da ayyukan raya ƙasa a jihar.
Kazalika, ya ce gwamnatin za ta ci gaba da ba da taimako ga harkokin na noma da Sauran ɓangarorin raya ƙasa ga al’ummar jihar ta Yobe.