Tinubu zai gudanar da salla ƙarama a Legas

Shugaban zai bar Abuja a ranar Lahadi, inda zai tafi Legas don yin bikin salla ƙarama.

Tinubu zai gudanar da salla ƙarama a Legas

Shugaba Bola Tinubu zai tashi daga Abuja, Babban Birnin Tarayya, zuwa Legas a ranar Lahadi don gudanar da bikin salla ƙarama.

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale ne, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.

Sanarwar ta ce: “Dangane da bukukuwan da ake yi, wanda ke nuna ƙarshen watan Ramadan, shugaban ƙasa zai gudanar da bikin salla tare da iyalansa.

Sanarwar ta kuma ce, “Shugaban kasa zai ci gaba da gudanar da ayyukansa a lokaci da kuma bayan salla.”