Tinubu zai halarci bikin rantsar da Ramaphosa a Afrika Ta Kudu
Za a sake rantsar da Shugaba Ramaphosa wa’adi na biyu bayan lashe babban zaɓen ƙasar.
Shugaba Bola Tinubu zai bar Legas zuwa birnin Pretoria na ƙasar Afirka ta Kudu, domin halartar bikin rantsar da shugaban ƙasar, Cyril Ramaphosa.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Tinubu, Ajuri Ngelale, ya fitar a ranar Litinin.
- Sudan na iya fuskantar yunwa mafi muni — Amurka
- Gwamnatocin baya ne suka jefa Najeriya cikin matsi — Onanuga
Ya ce shugaba Tinubu zai dawo Najeriya bayan kammala bikin rantsuwar.
Bikin rantsar da shugaba Ramaphosa, ya biyo bayan sake zaɓensa da aka yi a matsayin shugaban ƙasar karo na biyu.
A ranar Juma’a ne, aka sake zaɓen Ramaphosa wa’adi na biyu bayan jam’iyyarsa ta ANC ta haɗa gwamnatin haɗin gwiwa da ba a taɓa irin ta ba a ƙasar.
’Yan majalisar dokoki a birnin Cape Town sun kaɗa ƙuri’ar amincewa da shugaba Ramaphosa, mai shekara 71 a duniya, ya sake komawa kan karagar mulki na tsawon shekara biyar, bayan babban zaɓen ƙasar da aka gudanar a ranar 29 ga watan Mayu, ba tare da an samu wanda ya lashe zaɓen ba.
“Saboda haka na ayyana M.C. Ramaphosa a matsayin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa,” in ji alƙalin alƙalai Raymond Zondo, bayan ayyana sakamakon zaɓen ƙasar.
Zaɓen na watan da ya gabata ya kawo sauyi mai cike da tarihi ga Afirka ta Kudu, wanda ya kawo ƙarshen mulkin shekara 30 da marigayi Nelson Mandela ya yi.
Jam’iyyar Mandela ta jagoranci gwagwarmayar kawo ƙarshen mulkin wariyar launin fata, inda ta samu kashi 40 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa, kuma a karon farko ta rasa cikakken rinjaye a majalisar dokokin ƙasar.
Daga nan ta ƙulla yarjejeniya wajen kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa.