Tinubu zai halarci bikin rantsar da sabon shugaban kasar Senegal

Ana sa ran Tinubu zai dawo Najeriya da zarar an kammala bikin rantsuwar.

Tinubu zai halarci bikin rantsar da sabon shugaban kasar Senegal

Shugaban Kasa, Bola Tinubu zai tashi daga Abuja a ranar Talata zuwa Senegal, domin halartar bikin rantsar da sabon shugaban kasar, Bassirou Diomaye Faye.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale ne, ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.

Ya ce Tinubu zai halarci rantsuwar ne, biyo bayan gayyatar da Senegal ta yi masa.

Tinubu, wanda shi ne Shugaban Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afrika (ECOWAS), zai bi sahun shugabannin kasashen Afirka domin halartar bikin da za a yi a ranar Talata.

Shugaba Tinubu zai samu rakiyar ministan harkokin kasashen waje, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar da wasu manyan jami’an gwamnati.

Sanarwar ta ce ana sa ran shugaba Tinubu zai dawo Najeriya da zarar an kammala rantsar da sabon shugaban na Senegal.

Muhimman batutuwa da Biden ya taɓo a jawabin yi wa Amurkawa bankwana

IPMAN ta musanta batun ƙara farashin man fetur

Gwamnatin Tinubu ta yi wa Sarki Sanusi raddi

Ɗan shekara 85 ya yi wa ’yar shekara 4 fyaɗe