Tinubu zai halarci jana’izar mahaifiyar Shugaban Jam’iyyar APC a Filato
Tinubu zai koma Legas da zarar an kammala jana’izar.
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, zai tashi daga Legas zuwa Jos, Babban Birnin Jihar Filato, a ranar Asabar domin halartar jana’izar mahaifiyar Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Farfesa Nantewe Yilwatda Goshwe.
Zai halarci jana’izar Nana Lydia Yilwatda Goshwe, mahaifiyar Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa.
- Ana fargabar mutuwar mutane a gobarar tankar mai
- Boko Haram ta wuce yadda mutane ke tsammani — Jonathan
Bayo Onanuga, Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Tsare-tsare, ya ce Shugaban Ƙasa zai kuma gana da shugabannin coci daga Arewacin Najeriya a Jos.
Ana sa ran Tinubu zai koma Legas a ranar bayan kammala ziyarar.
A gefe guda kuma, Ma’aikatar Yaɗa Labarai ta Jihar Filato ta sanar da taƙaita zirga-zirgar ababen hawa a Jos da Bukuru saboda ziyarar TIinubu.
Kwamishinan Yaɗa Labarai, Rt. Hon Joyce Lohya Ramnap, ya ce za a rufe wasu manyan hanyoyi daga ƙarfe 7 na safiyar ranar Asabar domin bai wa tawagar Shugaban Ƙasa damar yin zirga-zirga ba tare da matsala ba.
Hanyoyin da abin zai shafa sun haɗa da:
1. Mararaban Jama’a zuwa babbar hanyar Bukuru
2. Dadin-Kowa, Tsohon Filin Jirgi zuwa shataletalen Filato
3. Shataletalen Hillstation zuwa Hedikwatar COCIN/Central Bank road
Gwamnati ta roƙi al’umma da masu ababen hawa su yi haƙuri tare da haɗin kai, inda ta bayyana waɗannan matakan a matsayin na wucin gadi don tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali yayin ziyarar.