Tinubu zai halarci taron ECOWAS a Guinea-Bissau
Wannan shi ne karo na biyu da shugaban kasar zai halarci taro a kasashen waje tun bayan rantsar da shi.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai halarci taron shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS karo na 63 da za a gudanar a kasar Guinea-Bissau.
A wata sanarwa da mai bai wa shugaban kasar shawara kan ayyukan na musamman Dele Alake ya fitar, ya ce shugaban zai bar Najeriya a yau Asabar domin halartar taron wanda za a gudanar ranar Lahadi.
- Tinubu zai biya bashin takardun lamunin ƙasashen waje a watan Yuli
- Hajiyar Najeriya mai shekara 66 ta rasu bayan kammala Aikin Hajji
Sanarwar ta ce shugaban zai samu rakiyar wasu daga cikin masu ba shi shawara tare da wasu manyan jami’an gwamnatinsa.
Ana sa ran tattauna muhimman batutuwan da ke damun kasashen kungiyar ciki har da matsalar tsaro da kasashen yankin ke fuskanta, tare da yin nazari kan rahoton da majalisar ministocin kungiyar suka fitar a taronsu na 90 da suka gudanar.
Haka kuma akwai batun huldar kasuwanci tsakanin kasashen Afirka tare da yin nazari kan batun mika mulki hannun farar hula a kasashen Mali da Burkina Faso da kuma Guinea.
Sauran batutuwan da ake sa ran taron zai tattauna sun hadar da batun kudin bai daya na kungiyar, da matsalar da ake samu wajen safarar kayayyaki tsakanin wasu kasashen yankin.
Wannan shi ne karo na biyu da shugaban kasar zai halarci taro a kasashen waje tun bayan rantsar da shi a matsayin shugaban kasar ranar 29 ga watan Mayu.
Taro na farko da Tinubu ya halarta a kasashen waje, shi ne taron harkokin kudi da ya gudana a Faransa cikin watan Yuni.
Ana sa ran shugaban kasar zai koma Najeriya bayan kammala taron.