Tinubu zai je Saudiyya taron kasashen Larabawa da Afirka

Ana sa ran shugaban zai yi jawabi game da sha’anin tattalin arziki da kuma yaki da ta’addanci.

Tinubu zai je Saudiyya taron kasashen Larabawa da Afirka

Tinubu zai yi balaguro

Shugaba Bola Tinubu, zai kai ziyara birnin Riyadh na Kasar Saudiyya domin halartar taron kasashen Larabawa da Afirka a ranar 10 da 11 ga watan nan na Nuwamba.

Mai magana da yawun shugaban, Ajuri Ngelale, ya ce a yayin taron, Tinubu zai tattauna kan batutuwa da suka shafi huldar tattalin arziki tsakanin yankunan da harkar noma da kuma yaki da ta’addanci.

Sauran su ne batun inganta harkokin kasuwanci da zuba jari a tsakanin Saudiyya da nahiyar Afirka.

A cewarsa hadimin shugaban kasar, halartar taron wani yunkuri ne na  bunkasa tattalin arzikin Najeriya da kuma jawo hankalin kasashen waje.

Ngelale ya ce a matsayin Tinubu na shugaban hukumar gudanarwar Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Yammacin Afirka (ECOWAS) zai kasance kan gaba a taron wajen bayar da shawarwarin zurfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen yankuna biyu.

“Tabbas, Shugaba Tinubu, yana da matukar son ganin Najeriya a yanayin da za ta iya amfani da damarmakin da za a samu ta hanyar aiwatar da yarjejeniyar ciniki cikin ’yanci a nahiyar Afirka.

“Hukumar Tattalin Arziki ta Majalisar Dinkin Duniya na hasashen a zuwa shekarar 2050 da kasuwanci a nahiyar zai haura Dala tiriliyan 29,” in ji hadimin shugaban kasar.