Tinubu zai kashe tiriliyan 1.5 wajen gina layin dogo na zamani a birnin Kano
Gwamnatin Tarayya za ta kashe Naira tiriliyan daya da rabi don gina layin dogo na zamani domin saukaka harkar sufuri a cikin birnin Kano.
Layin dogo na zamani a Abuja
Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar Wakilai, Abubakar Kabir Abubakar, ya ce Gwamnatin Tarayya za ta kashe Naira tiriliyan daya da rabi don gina layin dogo na zamani domin saukaka harkar sufuri a cikin birnin Kano.
Ya bayyana hakan ne lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a Kano, inda ya ce aikin zai saukaka wa mazauna birnin wahalar da suke sha a harkar sufuri.
- Zamfarawa sun yi zanga-zanga kan hare-haren ’yan bindiga
- Abba ya yi alhinin hadiminsa da ’yan daba suka kashe a Kano
Ya ce, “Wannan aikin na gina layin dogo na zamani ya kai Dalar Amurka biliyan daya, kwatankwacin Naira tiriliyan daya da rabi.
“Ga wadanda suke tafiye-tafiye zuwa kasashen waje, musamman kasashen Turai da nahiyar Asiya, sun san akwai irin wadannan ayyukan kuma suna da muhimmanci. Aikin zai kara habaka tattalin arzikin jihar idan aka kammala shi.”
Dan majalisar ya kuma ce sabanin yadda ake yadawa, Shugaban Kasa Bola Tinubu, ya bullo da muhimman ayyukan raya kasa a bangarorin lafiya da aikin gona da ilimi da kuma tsaro a Arewacin Najeriya.
“Abin mamaki ne idan na ji wasu mutane na cewa Shugaba Tinubu bai damu da Arewa ba. Ni ne shugaban kwamitin kasafin kudi, kuma na san me ya yi wa Arewa.
“Ya kamata mu ajiye son rai a gefe guda mu fada wa kanmu gaskiya a kan Shugaba Tinubu. Ya bijiro da ayyuka da dama a Arewa da ya kamata a yaba masa,” in ji Abubakar Bichi.