Tinubu zai kayar da Kwankwaso da Abba a Kano a zaben 2027 —Abdullahi Abbas

Abdullahi Abbas ya ce APC za ta samu ninki uku na kuri’un 2023 a zabe mai zuwa a Kano, amma Abba da Kwankwaso za su kai labari ba a zaben 2027

Tinubu zai kayar da Kwankwaso da Abba a Kano a zaben 2027 —Abdullahi Abbas

Tinubu da Kwankwaso

Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kano, Abdullahi Abbas, ya jaddada cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf da jagoran Jam’iyyar NNPP na kasa, Rabi’u Musa Kwankwaso, za su sha kaye a jihar a zaben 2027.

Abdullahi Abbas ya cewa Kwankwaso ba shi da farin jinin lashe zaben shugaban kasa 2027, shi kuma Gwamna Abba zai sha kaye ne saboda dibar karan mahaukaciya suka yi wa harkokin mulkin jihar.

Shugaban na APC ya kuma bugi kirji da cewa a zaben 2027 Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai samu ninki uku na kuri’un da ya samu a jihar a 2023.

Furucin nasa na zuwa ne a martaninsa ga takwaransa na NNPP na Jihar Kano, Hashimu Dungurawa, wanda ya ce rikicin masarautun jihar zai yi mummumar illa ga Shugaba Tinubu a zabe 2027.

Abdullahi Abbas ya bayyana baka ne a martaninsa ga takwaransa na NNPP, Hashimu Dungurawa, wanda ya ce rikicin masarautun jihar zai sa shugaban kasar faduwa zaben a jihar a 2027.

Amma Abbas a wata sanarwa ranar Litinin a Abuja,  ya ce a yanzu Jam’iyyar APC ta kara hade kai da farin jini kuma za ta kawo ninku uku na kuri’un da ta samu a zaben shugaban kasa da ya gabata a Kano.

“Rikicin neman karbuwa da ya dabaibaye NNPP mai cike da rabuwar kai a NNPP Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da jagoranta, abin kunya ne.

“Hakan ya fallasa mummunar gazawarta, duk da cewa tana takama da neman shugabancin kasa a shekarar 2027.

“Muna tabbatar wa shugabanmu da shugabancin jam’iyyar ta ƙasa cewa yanzu APC ta Jihar Kano ta kasa samun haɗin kai da farin jini kuma a kullum tana jan hankalin mutane masu kima da siyasa a cikinmu.

“Mun shirya kuma za mu kwao fiye da ninki uku na kuri’un da muka samu a zaben shugaban kasa na 2023.

“Bayan yadda jama’a suka shdai gazawar gwamnatin NNPP karkashin jagorancin Gwamna Abba Yusuf a jihar Kano a cikin shekara guda, yadda jam’iyyar ke haddasawa da kuma daukar nauyin rikici da wasu manufofinsa na masu illla ga jama’a, abubuwa ne da masu zabe za su yi la’akari da su a zabe mai zuwa.

“Sanin kowan ne cewa gwamnonin wasu jihohi sun kaddamar ayyukan ci gaba a bikin cikarsu  shekara guda a kan karagar mulki, amma Gwamnatin Kano ta NNPP ta shagaltu da karkatar da al’ummar jihar daga gazawarta ta a wannan bangare,ta hanyar fakewa da dokar masarautu mai cike da rudani,” in ji shugaban nan APC.