Tinubu zai ranto bashin dala biliyan daya a Bankin Raya Kasashen Afirka

Bankin raya ƙasashen Afirka da zai ba da rancen, za a biya a cikin shekara ashirin da biyar.

Tinubu zai ranto bashin dala biliyan daya a Bankin Raya Kasashen Afirka

Majalisar Zartarwa ta amince da karbo lamunin gata na dala biliyan daya daga Bankin Raya Kasashen Afirka AfDB, a cewar Ministan Kuɗi Olawale Edun.

Edun ya shaida wa manema labarai hakan ne bayan taron Majalisar Zartawar da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya jagoranta ranar Litinin.

A cewar ministan, bashin wanda za a yi amfani da shi wajen cike gibin Kasafin Kudin 2024, akwai kudin ruwa kashi 2.4.

Kazalika, ya ce Bankin raya ƙasashen Afirka da zai ba da rancen, za a biya a cikin shekara ashirin da biyar, amma akwai daga kafa na shekara takwas idan lamunin ya wuce ba a biya ba.

“Majalisar Zartarwa ta amince da wani rancen rangwame na dala biliyan daya don tallafa wa kasafin kudin kasar gaba daya da kuma amfani da shi wajen inganta samar da kudaden waje a kasar,” in ji Edun.

A gobe Laraba ce ake sa ran Shugaba Tinubu zai gabatar da kudurin Kasafin Kuɗin ga Majalisar Dokokin Tarayya don neman amincewar ’yan majalisar.