Tinubu zai tafi Amurka taron Majalisar Dinkin Duniya

Tinubu zai gana da takwarorinsa na Amurka, Comoros da Afirka ta Kudu.

Tinubu zai tafi Amurka taron Majalisar Dinkin Duniya

A ranar Lahadi ake sa ran Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu zai yi balaguro zuwa Amurka domin halartar taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 78 da zai gudana daga ranar 18 zuwa 26 ga watan Satumba.

Mai magana da yawun Shugaban Kasar, Cif Ajuri Ngelale ne ya sanar da hakan a wannan Juma’ar yayin yi wa manema labarai karin haske dangane da babban taron wanda shugabannin duniya za su halarta.

A gefe guda, Shugaba Tinubu zai kuma aiwatar tare da halartar wasu muhimman lamurra da za su su shafi tattalin arzikin Najeriya.

A cewar Ngelale, Tinubu zai tattauna da wasu shugabannin manyan kamfanoni masu nasaba da tattalin arziki, ciki har da shugaban Kamfanin Fasahar Zani na Microsoft, Brad Smith, domin bunkasar tattalin arzikin a fagen fasahar sadarwa.

Ngelale ya kara da cewa, Shugaban Kasar zai kuma gana Sir Nick Clegg, Babban Jami’in Zartarwa na Kamfanin Sadarwa na Meta Technologies, domin ribato wa Najeriya sabbin tsare-tsare a fagen fasahar na’urori masu aiki da tunani.

Kazalika, Tinubu zai gana da Babban Shugaban Kamfanin Lantarki da suka shafi makamashi, sufurin jiragen sama da makamantansu.

Ngelale ya ci gaba da cewa, Shugaba Tinubu zai gana da Shugaban Kamfanin Mai na ExxonMobil domin bunkasa harkokin zuba jari a bangaren man fetur da iskar gas.

Baya ga wannan, Tinubu zai gabatar da jawabai na musamman a yayin Babban Taron na Majalisar Dinkin Duniya musamman kan abin da zai shafi kasashe masu tasowa wajen sauya fasalin tsare-tsaren kudi a duniya baki daya.

Ngelale ya ce, Tinubu zai gana da takwarorinsa na Amurka, Comoros da Afirka ta Kudu.

Haka kuma, Tinubu zai gana da Shugaban Hukumar Tarayyar Turai da Firaministan Netherlands da Sarkin Jordan da takwarorinsa na Brazil da Algeria da kuma Firiministan Sifaniya.

Aminiya ta ruwaito cewa, taron Majalisar Dinkin Duniya na bana zai mayar da hankali kan yaukaka dangartaka da aminci a tsakanin kasashen duniya.