Tinubu zai tafi Dubai taron sauyin yanayi ranar Laraba

Tinubu zai gabatar da jawabi a taron wanda zai gudana tsakanin ranakun 1 da 2 ga watan Disamba.

Tinubu zai tafi Dubai taron sauyin yanayi ranar Laraba

Tinubu zai yi balaguro

Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai yi balaguro a ranar Laraba zuwa birnin Dubai na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa domin halartar taron sauyin yanayi na COP28.

Wata sanarwa da ta fito daga hannun mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale, a yau Talata, ta ce Tinubu zai gabatar da jawabi a taron wanda zai gudana tsakanin ranakun 1 da 2 ga watan Disamba.

Bayanin da shugaba Tinubu zai gabatar lokacin taron zai mayar da hankali ne kan matsayar Najeriya game da sauyin yanayi, musamman abin da ya shafi amfani da makamashi maras gurɓata muhalli da kuma samar da kuɗi kan ayyukan daƙile ɗumamar yanayi.

Ana sa ran Tinubun zai yi amfani da damar wajen neman ƙasashen da suka ci gaba da su ƙara tallafa wa ƙasashe masu tasowa wajen yaƙi da sauyin yanayi.

Haka nan Tinubu zai yi amfani da lokacin taron wajen ganawa da masu ruwa da tsaki da nufin janyo ra’ayinsu wajen zuba jari domin samar da aikin yi a Najeriya.