Tinubu zai tafi Ghana rantsar da John Mahama

Za a rantsar da John Mahama a ranar Talata.

Tinubu zai tafi Ghana rantsar da John Mahama

Shugaba Bola Tinubu, zai bar Abuja a ranar Litinin zuwa Accra, Babban Birnin Ghana, domin halartar bikin rantsar da sabon shugaban ƙasar, John Dramani Mahama, a ranar Talata.

John Mahama, wanda ya taɓa yin shugabancin Ghana daga 2011 zuwa 2017, ya sake lashe zaɓen shugaban ƙasar a watan Disamban 2024.

Mahama zai gaji Shugaba Nana Akuffo-Addo, wanda yake kan mulki tun shekarar 2017.

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya ce Mahama ne da kansa ya gayyaci Tinubu, wanda ya ziyarci Najeriya a watan Disamban 2024.

Onanuga, ya bayyana cewa akwai kyakkyawar alaƙa ta kashin kai tsakanin shugabannin biyu, tare da danƙon zumunci tsakanin Najeriya da Ghana.

Tinubu, wanda shi ne shugaban ƙungiyar ECOWAS, zai shiga sahun sauran shugabannin Afrika a wajen halartar bikin.

Zai samu rakiyar Ministar Harkokin Wajen, Bianca Odumegwu-Ojukwu, da wasu manyan jami’an gwamnatinsa.

Boko Haram ta mamaye sansanin sojoji ta sace makamai a Borno

Ɗan ta’adda ya sa wa Zamfarawa harajin N100m

An kori jami’an EFCC 27 daga aiki da saboda almundahana

Gwamnan Bauchi ya sallami Kwamishinoninsa