Tinubu zai tafi taron AU a Kenya
Shugaba Tinubu zai samu rakiyar manyan jami’an gwamnatinsa.
Shugaba Bola Tinubu zai yi tafiya zuwa birnin Nairobi na kasar Kenya domin halartar taron tsakiyar shekara na gamayyar kungiyoyin hadin kan Afirka da na rassan kungiyoyin tattalin arzikin kasashen yankin Afirka.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban Kasar, Dele Alake ya fitar, ya ce shugaban zai bar Najeriya ranar Asabar domin halartar taron da zai gudana ranar Lahadi 16 ga watan Yuli.
- Jaruman Hollywood sun tsunduma yajin aiki karon farko cikin shekaru 63
- Ya kamata a tura karin dakaru iyakokin Najeriya — Majalisar Wakilai
Shugaba Tinubu zai bi sahun sauran takwarorinsa shugabannin kasashen da ministocin harkokin wajen kasashen Afirka da sauarn manyan bakin da za su halarci taron.
A matsayinsa na shugaban kungiyar ECOWAS, Tinubu zai gabatar da rahoton irin ci gaban da kungiyar ta samu cikin wata shida da suka gabata, a fannin harkokin da suka shafi kasuwanci da walwala da zuba jari da samar da abubuwan more rayuwa da zaman lafiya da tsaro tsakanin kasashen yankin.
Sauran rassan kungiyoyin tattalin arzikin kasashen Afirkan da za su halarci taron sun hadar da ECOWAS da kungiyar kasashen gabashin Afirka ta ECA da Kungiyar Kasuwancin bai ɗaya ta kasashen gabashi da Kudancin Afirka (COMESA) da kungiyar kasashen Kudancin Afirka ta (SADC) da kungiyar kasashen yankin Sahel, da kungiyar kasashen yankin Magrib da kungiyar tattalin arzikin kasashen tsakiyar Afirka ta kungiyar IGAD.
Shugaba Tinubu wanda zai samu rakiyar manyan jami’an gwamnatinsa, zai dawo Najeriya da zarar an kammala taron, kamar yadda sanarwar ta bayyana.