Tinubu zai tafi taron makamashi a Tanzania
Tinubu zai bayyana himmar Nijeriya wajen samar da wutar lantarki da rawar da ƙasar ke takawa wajen ci gaban makamashi a Afirka.
A gobe Lahadi ake sa ran Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai bar Abuja zuwa birnin Dar es Salaam da ke a ƙasar Tanzaniya.
Shugaban zai yi balaguron ne domin halartar taron shugabannin Afirka kan makamashi a ranar 27 zuwa 28 ga Janairu, 2025.
Mai ba Shugaba Tinubu shawara kan watsa labarai, Bayo Onanuga, ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar.
Gwamnatin Tanzania tare da haɗin gwiwar Babban Bankin Raya Afirka da Bankin Duniya ne za su dauki nauyin taron, a cewar kakakin Tinubu.
Onanuga ya ce taron zai mayar da hankali kan bunƙasa shirin nan na “Mission 300” domin samar wa mutane miliyan 300 wutar lantarki a Afirka zuwa shekarar 2030.
A birnin Dar es Salaam, shugabannin Afirka, shugabannin kamfanoni masu zaman kansu, da kungiyoyin fararen hula za su tattauna dabarun ƙara samun wutar lantarki a nahiyar.
Sanarwar ta ce taron zai zama dandamali na musayar ilimi, ƙwarewa, da albarkatu don magance matsalolin makamashi a Afirka.
Sanarwar ta ƙara da cewa taron zai mayar da hankali kan samar da wuta a yankunan karkara, sabunta manufofin makamashin, amfani da makamashi mai inganci, da jawo kamfanoni masu zaman kansu don zuba jari.
“A rana ta farko, ƙasashen da za su halarta, ciki har da Nijeriya, za su gabatar da dabarun cimma samar da wuta ga ’yan ƙasarsu cikin shekaru biyar.
“A rana ta biyu, shugabannin ƙasashen za su rattaba hannu kan yarjejeniyar makamashi ta Dar es Salaam, wacce za ta bayyana hanyar da za a bi don cimma burin ‘Mission 300’.”
Shugaba Tinubu zai yi jawabi don tabbatar da himmar Nijeriya wajen samar da wutar lantarki ga kowa da rawar da ƙasar ke takawa wajen ci gaban makamashi a Afirka.
Kazalika, Tinubun zai bayyana ayyukan Nijeriya na samar da makamashi mai tsafta da dabarun inganta isar da wuta a nahiyar.
Tinubu wanda zai dawo gida Nijeriya da zarar an kammala taron, tawagarsa za ta ƙunshi Ƙaramar Ministar Harkokin Waje, Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu, Ministan Wuta, Adebayo Adelabu, da mashawarcin shugaban kasa kan makamashi, Olu Verheijen, tare da wasu manyan jami’ai.