Tinubu zai tattauna da ’yan kwadago kan shirinsu na fita zanga-zanga 

Ministan kwadago, Simon Lalong ne ya sanar da hakan

Tinubu zai tattauna da ’yan kwadago kan shirinsu na fita zanga-zanga 

Shugabannin kwadago bayan tattaunawa da Tinubu

Gwamnatin Tarayya ta ce za ta tattauna da shugabannin kungiyoyin kwadago da misalin karfe 3:00 na ranar Litinin saboda kaucewa shiga zanga-zangarsu ranar Talata.

Ministan Kwadago, Simon Lalong, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da safiyar Litinin.

Ya ce bai kai ga zama da kungiyoyin kwadago ba kafin yau [Litinin], amma bai samu cikakkun bayanai daga sauran bangarorin da ya kamata ba.

Lalong ya kuma yi kira ga kungiyoyin kwadago na NLC da TUC da su roki abokan huldarsu don su dakatar da shirin zanga-zangar ba yanzu ba.

A makon da ya gabata ne dai NLC da TUC suka sanar da fara zanga-zanga ranar Talata domin sake matsa wa gwamnati lamba kan manufofinta na tattalin arziki da suka ce sun yi wa ’yan kasa tsauri.

Ɗan majalisa ya yi jinjina kan naɗa Danyaya Sarkin Ningi

’Yan Sanda sun kama gungun ’yan fashi 7 a Katsina

Zaɓen Edo: Ana ci gaba da ƙirga ƙuri’u

Zaɓen Edo: INEC ta tsawaita kaɗa ƙuri’a a wasu yankuna