Tinubu zai yanke hukuncin karshe kan jirgin Nigeria Air —Keyamo
Ministan ya ce batun jirgin na ‘Nigeria Air’ yana gaban shugaba Tinubu.
Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo ya sanar cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai yanke hukunci kan makomar kamfanin jirgin saman Najeriya Air.
Kaddamar da jirgin Nigeria Air da aka yi kafin shudewar gwamnatin Buhari ya bar baya da kura inda aka gano jirgin kamfanin da ya sauka a filin jiragen sama na Abuja hayarsa aka dauko daga Ethiopian Airlines.
- Tinubu zai je Saudiyya taron kasashen Larabawa da Afirka
- Sarkin Kano ya je ta’aziyyar basaraken Kasar Ibira a Kogi
Najeriya ta zabi Kamfanin Jiragen Sama na kasar Habasha a matsayin abokin hadin gwiwar Nigeria Air, sai dai wannan lamari bai yi wa mutane da dama dadi ba.
A makon da ya gabata ne dai kamfanin Ethiopian Airlines ta hannun shugabansa, Mesfin Tasew ya ce gwamnatin da ta shude ce ta bukaci a yi wa jirgin Ethiopian Airlines fentin tambarin Nigeria Air.
Da aka tambaye shi kan matsayin kamfanin na Nigeria Air, Keyamo ya ce batun yana kan teburin shugaban kasa domin yanke hukunci.
Da yake magana kan batun Hadaddiyar Daular Larabawa da Najeriya, ya ce, “Muna aiki ta bayan fage haikan. Zan je Dubai na da makonni biyu masu zuwa don tattauna wasu batutuwa da mahukuntar kasar.