Tinubu zai sallami wasu ministocinsa
Tinubu ya umarci ministocin da su daina jin kunyar yin magana da kafofin yaɗa labarai.
Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana ƙudirin yi wa majalisar ministocinsa sauye-sauye nan ba da jimawa ba.
Mai magana da yawun Shugaban Kasa, Bayo Onanuga ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa a ranar Laraba a Abuja.
- Muna so a yafe wa Nijeriya basussuka —Kashim Shettima
- Majalisa ta tabbatar da naɗin Kekere-Ekun a matsayin Alƙalin Alƙalan Najeriya
Ya kara da cewa, sabanin yadda ake tsegume-tsegume a wasu bangarori, gwamnati mai ci ta samu gagarumar nasara a yunƙurinta na kawo sauyi ga tattalin arzikin ƙasar, wanda jama’a ba su da masaniya a kai.
Onanuga ya ce Shugaba Tinubu ya umarci ministocinsa da su tabbatar sun shiga cikin jama’a ta hanyar bayyana abubuwan da gwamnati ke yi a ma’aikatunsu daban-daban.
Ya ce, “Ban san a wane lokaci za a yi ba amma dai ya bayyana muradinsa na yin garambawul a majalisar ministocinsa kuma zai yi.
“Ban sani ba ko zai yi hakan kafin 1 ga watan Oktoba amma dai tabbas zai yi..bai faɗa mana lokaci ba dai,” inji Onanuga.
Mista Onanuga ya ce shugaban ya kuma umarci ministocin “da su daina jin kunyar yin magana da kafofin yaɗa labarai domin tallata ayyukan gwamnatin.”
A cewarsa: “Wasu daga cikinsu na gudun magana a talabijin, ko rediyo. Ya nemi su daina yin hakan, su fita su bayyana ayyukan da suke yi.”