Tinubu zai zarce Afirka ta Kudu daga Faransa
Ana sa ran cewa a gobe Litinin Shugaban Najeriya Bola Tinubu zai zarce birnin Cape Town na ƙasar Afirka ta Kudu daga Faransa. Wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban Kasa Bayo Onanuga ya fitar ta ce Tinubu zai zarce Afirka ta Kudu domin jagorantar taron Hukumar Ƙasashen Biyu ta BNC karo na 11 […]
Ana sa ran cewa a gobe Litinin Shugaban Najeriya Bola Tinubu zai zarce birnin Cape Town na ƙasar Afirka ta Kudu daga Faransa.
Wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban Kasa Bayo Onanuga ya fitar ta ce Tinubu zai zarce Afirka ta Kudu domin jagorantar taron Hukumar Ƙasashen Biyu ta BNC karo na 11 tare da Shugaba Cyril Ramaphosa.
- Wanda ya auri ’yar tsana shekaru 6 har yanzu yana son matarsa
- Ba don ni ba da Abacha ya kashe Obasanjo — Gowon
Gabanin taron da zai gudana a ranar Talata, 3 ga watan Disamba, Tinubu da takwaransa za su halarci taron ministoci da zai gudana a ranar Litinin a Zauren Majalisar Tarayyar Afirka ta Kudu da ke Cape Town.
Shugabannin za su tattauna kan wasu muhimman batutuwa da suka shafi dangartakar ƙasashen biyu da suka haɗa siyasa, kasuwanci, tsaro, baƙin haure, haƙar ma’adanan ƙasa, jakadanci, cinikayya da sauransu.
Mista Onanuga ya ce tun a ranar 20 ga watan Yunin bana ne shugabannin biyu suka yi sharar fagen dangane da taron a birnin Johannesburg, inda na wannan karon zai yi bitar wanda ya gabace shi da aka gudanar a tsakanin 29 ga watan Nuwamba zuwa 1 ga Disamban 2021 a Abuja.
A shekarar 1999 ce aka ƙirƙiri Hukumar Ƙasashen biyu domin inganta alaƙar da ke tsakanin ƙasashen biyu, inda taron farko tsakanin shugabannin ƙasashen biyu ya gudana a watan Oktoba na 2019 a Pretoria.
An ƙirƙiri hukumar ta BNC domin bunƙasa harkokin diplomasiyya, tattalin arziki, cinikayya, tsaro da sauransu.