Tinubu zai zarce Landan daga Faransa — Fadar Shugaban Kasa

An yi tsammanin dawowarsa Abuja a yau Asabar, amma wata tafiyar ta taso a cewar Fadar Shugaban Kasa.

Tinubu zai zarce Landan daga Faransa — Fadar Shugaban Kasa

Tinubu

Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, wanda aka yi tsammanin dawowarsa Abuja a yau Asabar, yanzu zai wuce birnin Landan na kasar Birtaniya, domin wata gajeriyar ziyarar ta kashin kai.

Dele Alake, mai bai wa Shugaban Kasa shawara na musamman kan ayyukan sadarwa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar.

Alake ya ce shugaban zai dawo Najeriya nan da wani lokaci gabanin bikin Babbar Sallah da za a gudanar a ranar Laraba mai zuwa.

Aminiya ta ruwaito cewa, Shugaba Tinubu ya bi sahun takwarorinsa na duniya wajen halartar taron sauyin yanayi da tattalin arziki wanda aka kammala ranar Juma’a a birnin Paris na kasar Faransa.

Mai magana da yawun shugaban kasar ya ce baya ga halartar taron da ya wakilci Najeriya da kyau, Shugaba Tinubu a gefe guda ya kuma gudanar da manyan tarurruka tare da takwarorinsa na kasashe da gwamnatoci da shugabannin ‘yan kasuwa na duniya da shugabannin manyan cibiyoyin hada-hadar kudi da raya kasa daga sassan duniya.

Ya kara da cewa, taron ya bai wa Shugaba Tinubu damar gabatar da shawarwarinsa na fadada fannin hada-hadar kudi, tabbatar da adalci ga nahiyar Afrika, da kuma gaggauta magance matsalolin da suka shafi talauci da sauyin yanayi.

NLC ta yi watsi da ƙara kuɗin kiran waya da data

DSS ta gurfanar da Mahdi Shehu kan zargin ta’addanci

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda